YADDA AKE SAMUN NAMIJI KO MACE A LOKACIN JIMA’I – Sheikh Dr Ahmad Gumi

In this video

A cikin wannan karatun Malam yayi bayani game da Hadisin da Muslim ya ruwaito da wani Bayahude yazo yayi masa tambayar da babu wanda ya san amsarta a wannan lokacin idan ba Annabin Allah ba se wani mutum daya ko biyu.

Amsar da Manzon Allah SAW ya bashi ya tabbatar da cewar shi manzon ne, amma Manzon Allah ya ce kafin wannan mutumin yayi masa tambayar be san amsar ba.

Akwai wadansu ilimomi game da yadda ake samun da namiji ko mace a lokacin saduwa.

Amsar da Manzon Allah Ya bayar a wancan lokacin, ilimin kimiyya ya gaskata shi.

(Visited 4,299 times, 1 visits today)