MATAN DA BAI KAMATA AYI MUSU KISHIYA BA – Dr. Ahmad Gumi

In this video

A cikin amsa da malam ya bayar game da mas’alar Maryam Sanda da kuma yadda mata suke kokarin kashe mazajensu idan suka samu labarin zasu kara aure, malam ya fadi irin hukuncin shari’ar musulunci ta tanada tare da kuma bayar da shawara idan mata basu daina wannan danyan hukuncin ba. A gefe guda Malam ya zargi mazaje da yin wawta wurin yin aurensu na farko da kuma rashin tantancewa daga wane gida zaka yi wannan auren da kuma tabbatar da cewar irin wannan matar ta hada wadansu ka’idoji da bai kamata a kara mata kishiya ba. Wannan karatu ne da Malam yayi a ranar Laraba 26/01/2020 a Masjid Attauheed inda yake fassara a cikin littafin Attalqeen Fi Fiqhil Maliky

(Visited 1,128 times, 1 visits today)