KAMA MAHADI SHEHU: BA KU DA BANBANCI DA BOKO HARAM – Dr. Ahmad Gumi

Bayan kamawa da tsare shi da suka yi na sama da kwanaki goma, ga kuma sarar macijiya da hana ayi masa magani, wannan shine kadan daga cikin irin halin da Malam Mahadi Shehu ya ke ciki bayan da ya binciko almundahanar kudade da gwamnatin Masari take yi da a fannoni da dama.

Malam a cikin karatunsa ya fadi irin halayya da irin mulkin kama karya da gwamnatin mutanen mu suke yi duk lokacin da suka sami mulki a hannunsu.

A ciki malam ya kalubalanci tun daga Shugaban Kasa zuwa kasa wani ya fito ya rantse da Allah cewar bai ci kudin haramun na gwamnati ba. Wannan karatu ne da Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya gabatar jiya Juma’a 20/04/1442AH – 04/12/2020 a wurin tafsirin gida.

(Visited 26 times, 1 visits today)