HAUSA VERSION: Hukunchin Azumi Shidda Na Watan Shawwal A Mazhabin Malikiyah – Sheikh Dr. Ahmad Gumi

Azumin Kwana Shidda a watan Shawwal a wurin Malikiyah Makaruhi Ne domin bai inganta ba a wurin magabata (Salaf), kodayake daga baya duk da rashin ingancin shi, akwai wadanda suka inganta hadisin domin basu amfani da aikin magabata wurin tantance hadisai.

Wannan shi ya kawo bambamce bambamce tsakanin ma’abota ilimi. Wadansu da gudun bidia wadansu na kwadayin lada. Sai dai gudun bidia yafi lada akan kwadayin wata falalar da bata ingata ba a magabata.

Saboda, haka mutun zai iya yin azumin nafila da neman falalarsa cikin kowane wata gwargwadon iyawarsa kamar yadda Malik ya ruwaito a muwwatta.

Allah Ya shiryar damu hanya madaidaiciya. Ameen.

(Visited 20 times, 1 visits today)