DR. AHMAD GUMI YA FITAR DA SAUTIN SHEKARU 7 DA WANI SOJA YA FADA MISHI NA KISAN KARE DANGI GA FULANI

Idan kuna bibiyar karatun Malam zaku ji malam yana yawan fadar cewa a shekarar 2015 wani soja ya same shi ya fada mishi irin ta’adi da kisan kare dangi da ake bin Fulani cikin daji ana yi musu.

Yau malam ya saki sautin domin jama’a su ji da kunnensu su gane cewar wannan wata irin dasisace da aka shukata wacce take fitar da kashe-kashe a wannan lokacin.

Duk da cewar abubuwan da Fulanin daji suke yi a yanzu na kidnapping da kashe mutane babu gaira babu dalili ya kamata jama’a su fahimci irin abinda jahili zai iya aikatawa na rashin imani idan ya kai makura.

Idan har soja wanda yake da ilimi da wayewa zai iya yin irin wannan ta’annati to ya kuke ganin Fulanin da suke cikin daji da ba’a basu Ilimin Addini da na zamani ba suka sami makami?

Wannan shine dalilin daya sa malam yace a shiga dajin nan a karantar da su, a nemi sulhu da su da kuma ayi musu afuwa a kuma jawosu a jiki domin da yin haka ne zasu daina wannan ta’adi kuma su rungumi zaman lafiya.

(Visited 60 times, 1 visits today)