CORONAVIRUS: NASIHA ZUWA GA DUKKAN MUSULMAI

Coronavirus wata irin cuta ce da asalinta dabbobi ke da shi, kuma take yaduwa a tsakanin dabbobinm, sai gashi yanzu haka ta fitini Duniya kasancewar ta shiga jikin dan adam kuma dan adam din yana yadata. A cikin wannan nasiha da Sheikh Dr. Ahmad Gumi yayi ya fitar da abin da addinin Musulunci ya ce game da bullar Annoba da kuma yadda ya kamata a tsare kai daga samun ta. Kasancewar wannan cutar tana somawa ne kamar da mura da atishawa da tari malam ya bayar da shawara ga mutane da su guji masallatai a lokacin da suka kamu da muta mai tari da atishawa.

(Visited 11 times, 1 visits today)